uhura / ha_mc1_val.json
ebayes's picture
Upload 30 files
597042a verified
raw
history blame
14.8 kB
[
{
"question": "Bakin sarakunan Katsina ya daidaita kan su ..",
"a": "gudu",
"b": "6oye",
"c": "tsaya",
"d": "huta",
"answerKey": "a",
"context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Garkuwar bauna ita ce",
"a": "kahonta",
"b": "Wuyanta",
"c": "goshinta",
"d": "Surarta",
"answerKey": "a",
"context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18] maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Yanzu tun abin nan Geda, me kike jira ba ki mayar da yarinyar nan ɗakinta ba?’’\nWa ya faɗi wannan magana a wasan ‘Bari Ba Shegiya Ba Ce’ na Zaman Duniya Iyawa Ne na Y. Ladan?",
"a": "Baban Tagudu",
"b": "Bawa",
"c": "Kofur",
"d": "Alhaji Mai Rokoki",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Theatre"
},
{
"question": "Wane ne Gumuzu a labarin?",
"a": "wanda ya ba da Umar",
"b": "uban Umar",
"c": "uban gyatumarsa",
"d": "uban Abdulkarim",
"answerKey": "a",
"context": "\"Ina cikin sakar zuci sai Gumuzu yajuyo gare ni ya ce,\"Umar, ga Abdulkarim ya roke ni arziki yana son ka. Son nan da yake maka ba wai ka zama bawansa ne ba.Yana so in ka dauka a ranka, ka ga za ka iya zama da shi ka zama ɗansa, gama ba shi da ɗa, ko ɗan dangi ma\nbabu a gare shi. Ni na yarda ku tafi tare da shi, yanzu yardarka ce kawai muke jira!\nBayan wannan, sai na ɗaga kai kawai ina duban nisan ƙasar su Adulkarim, kuma ina tunawa gyaturmata lara da rai ba ta ma san inda Allah ya shilla da ni ba.\n A wurin sai duniyan nan ta taru ta yimini baƙi ƙirin ban san sa'ad da hawaye ya zubo mini ba. Da ganin haka sai Abdulkarim ya tambaye ni wai ko ba ni son sa ne? Ni kuwa na amsa masa ba haka ba ne, ba ni so ne in rabu da kasarmu. In na bi shi yaushe zan dawo gida? Shi kuma ya ce mini kowace shekara in zai zo lallai zai zo da ni domin in duba mutanen ƙasarnmu.\n Nace, To, na yarda'. Don kada su ce na cika rashin kunya bayan kuwa da sun yabe ni. Bayan da aka gama wannan magana sarai na yarda, sai Gumuzu ya ce mini in koma gida. Da na tashi zan tafi sai Abdulkarim ya kawo kantu babba ya ba ni, game da waɗansu dabinai ƙeƙasassu waɗanda babu irinsu ga zaƙi.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Waƙar ‘Gadar Zare’ ta Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Da Da Na Yanzu na D. Abdulkadir ’yar ƙwar nawa ce?",
"a": "Biyar",
"b": "Uku",
"c": "Huɗu",
"d": "Biyu",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "A kalmar marubuciya, akwai ɗafi",
"a": "biyu",
"b": "ɗaya",
"c": "uku",
"d": "huɗu",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Me ya yi ajalin sarki da wazirin Kwararrafawa?",
"a": "Doki.",
"b": "Dokin wuya.",
"c": "Ciwon cibiya.",
"d": "Dokin kofa.",
"answerKey": "a",
"context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Wace kalma ke da wasula dogaye?",
"a": "Kakaki",
"b": "Ayaba",
"c": "Tumatir",
"d": "Akwati",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Grammar"
},
{
"question": "Yaushe aka sami isa Muri?",
"a": "Bayan amsar mulki daga[Maryam Sa2] hannun kantan",
"b": "Kafin kafa kamfani",
"c": "Kafin zuwan Turawa",
"d": "Bayan buɗe kanti",
"answerKey": "a",
"context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe, ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Wanne ne bare daga cikin magungunan da magori ke bayarwa?",
"a": "Laya",
"b": "Turare",
"c": "Sassaƙe",
"d": "Shafi",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Culture"
},
{
"question": "Babban amsa-amon waƙar ‘Mu Sha Falala’ ta Sarkin Zazzau Aliyu Ɗansidi a Waƙoƙin Hausa, shi ne",
"a": "-la",
"b": "-ca",
"c": "-ma",
"d": "-ba",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Abu na farko cikin ashirin da Waziri Aku ya faɗa wa ɗansa Fasih, a Magana Jari Ce Na III, na A. Imam, shi ne",
"a": "dangana ga Allah",
"b": "girmama jama’a",
"c": "lura da mutane",
"d": "taimakon mutane",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Literature"
},
{
"question": "‘Ya ɗan’uwa da ke fatawa a kan zancen, Tawakkali da du’ai wadda ba bidi’a. Da fassarar ƙaddara bisa yadda anka faɗi. Cikin kitabu da sunna wanda ba bidi’a. Ai ka yi fatawarka gun wannan da bai da sani, Kuma bai da hikima ta rarrabe mas’alar bidi’a.’ A waɗannan baitoci na ‘Waƙar Bidi’a’ ta Waƙoƙin Sa’adu Zungur ana yin gargaɗi ne kan",
"a": "neman bayani wurin masana",
"b": "ƙarancin malamai a yanzu",
"c": "fayyace ƙarya cikin gaskiya",
"d": "dacewar mai karatu ya yi fatawa",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Song"
},
{
"question": "Rokon arziki a labarin na nufin",
"a": "\nneman taimako ",
"b": "roƙo cikin lalama",
"c": "\nneman sadaka",
"d": "roo cikin lumana",
"answerKey": "a",
"context": "\"Ina cikin sakar zuci sai Gumuzu yajuyo gare ni ya ce,\"Umar, ga Abdulkarim ya roke ni arziki yana son ka. Son nan da yake maka ba wai ka zama bawansa ne ba.Yana so in ka dauka a ranka, ka ga za ka iya zama da shi ka zama ɗansa, gama ba shi da ɗa, ko ɗan dangi ma\nbabu a gare shi. Ni na yarda ku tafi tare da shi, yanzu yardarka ce kawai muke jira!\nBayan wannan, sai na ɗaga kai kawai ina duban nisan ƙasar su Adulkarim, kuma ina tunawa gyaturmata lara da rai ba ta ma san inda Allah ya shilla da ni ba.\n A wurin sai duniyan nan ta taru ta yimini baƙi ƙirin ban san sa'ad da hawaye ya zubo mini ba. Da ganin haka sai Abdulkarim ya tambaye ni wai ko ba ni son sa ne? Ni kuwa na amsa masa ba haka ba ne, ba ni so ne in rabu da kasarmu. In na bi shi yaushe zan dawo gida? Shi kuma ya ce mini kowace shekara in zai zo lallai zai zo da ni domin in duba mutanen ƙasarnmu.\n Nace, To, na yarda'. Don kada su ce na cika rashin kunya bayan kuwa da sun yabe ni. Bayan da aka gama wannan magana sarai na yarda, sai Gumuzu ya ce mini in koma gida. Da na tashi zan tafi sai Abdulkarim ya kawo kantu babba ya ba ni, game da waɗansu dabinai ƙeƙasassu waɗanda babu irinsu ga zaƙi.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "Fonisiya kasa ce da taƙe…..\n",
"a": "kusa da teku",
"b": "nesa da teku",
"c": "kusa da Romawa",
"d": "cikin ƙasar Latin",
"answerKey": "a",
"context": "Karanta wannan labari a natse, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye da shi.\n \nMutanen Fonisiya, ƙasar nan ta bakin teku kusa da Siiya su ne suka fara ƙago rubutun abacada kimanin shekaru 3,400 da suka wuce. Wato su suna amfani da baƙaƙe da wasula 22 ne wajen rubutunsu. Sai Romawa suka ɗauki samfurin rubutun Fonisiyawa bayan kimanin shekaru 1,000, suka tsara rubuta harshensu na Latin ta yin amfani da bakaken abacada 23. Turawa kuma su suka koyi salon yin amfani da abacada irin na Latin. Irin wannan rubutu na Latin wanda ake yin\namfani da shi wajen rubuta harshen Turanci shi ne a Hausa alke kira rubutun boko.\n A fasalin rubutu mai amfani da baƙaƙe da wasula kuma, sai rubutun Larabci wanda shi ma yake amfani da wadansu alamnomi masu wakiltar muryoyi ko saututtuka irin na abacada, amma waɗanda suke da fasali daban da irin na rubutun Latin (wato boko), domin shi rubutun Larabci ana fara yin sa ne daga dama ana tafiya hagu, kuna ana kyasta wasulla a kan baƙaƙen ne, maimakon jeranta baƙi da wasali da ake yi a rubun boko. Shi dai rubutun Larabci ana jin an fara amfani da shi ne kimanin shekaru 2000 da suka wuce.\n",
"grade": "SS3",
"preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
"category": "Reading comprehension"
},
{
"question": "‘‘Neman magana, an ce da ’",
"a": "gwauro, yaya iyali?",
"b": "malami, gardi",
"c": "wawa, uwarsa ta mutu",
"d": "ɓarawo ya gudu.",
"answerKey": "a",
"context": "",
"grade": "SS3",
"preamble": "",
"category": "Oral literature"
}
]