File size: 82,354 Bytes
597042a
 
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53
54
55
56
57
58
59
60
61
62
63
64
65
66
67
68
69
70
71
72
73
74
75
76
77
78
79
80
81
82
83
84
85
86
87
88
89
90
91
92
93
94
95
96
97
98
99
100
101
102
103
104
105
106
107
108
109
110
111
112
113
114
115
116
117
118
119
120
121
122
123
124
125
126
127
128
129
130
131
132
133
134
135
136
137
138
139
140
141
142
143
144
145
146
147
148
149
150
151
152
153
154
155
156
157
158
159
160
161
162
163
164
165
166
167
168
169
170
171
172
173
174
175
176
177
178
179
180
181
182
183
184
185
186
187
188
189
190
191
192
193
194
195
196
197
198
199
200
201
202
203
204
205
206
207
208
209
210
211
212
213
214
215
216
217
218
219
220
221
222
223
224
225
226
227
228
229
230
231
232
233
234
235
236
237
238
239
240
241
242
243
244
245
246
247
248
249
250
251
252
253
254
255
256
257
258
259
260
261
262
263
264
265
266
267
268
269
270
271
272
273
274
275
276
277
278
279
280
281
282
283
284
285
286
287
288
289
290
291
292
293
294
295
296
297
298
299
300
301
302
303
304
305
306
307
308
309
310
311
312
313
314
315
316
317
318
319
320
321
322
323
324
325
326
327
328
329
330
331
332
333
334
335
336
337
338
339
340
341
342
343
344
345
346
347
348
349
350
351
352
353
354
355
356
357
358
359
360
361
362
363
364
365
366
367
368
369
370
371
372
373
374
375
376
377
378
379
380
381
382
383
384
385
386
387
388
389
390
391
392
393
394
395
396
397
398
399
400
401
402
403
404
405
406
407
408
409
410
411
412
413
414
415
416
417
418
419
420
421
422
423
424
425
426
427
428
429
430
431
432
433
434
435
436
437
438
439
440
441
442
443
444
445
446
447
448
449
450
451
452
453
454
455
456
457
458
459
460
461
462
463
464
465
466
467
468
469
470
471
472
473
474
475
476
477
478
479
480
481
482
483
484
485
486
487
488
489
490
491
492
493
494
495
496
497
498
499
500
501
502
503
504
505
506
507
508
509
510
511
512
513
514
515
516
517
518
519
520
521
522
523
524
525
526
527
528
529
530
531
532
533
534
535
536
537
538
539
540
541
542
543
544
545
546
547
548
549
550
551
552
553
554
555
556
557
558
559
560
561
562
563
564
565
566
567
568
569
570
571
572
573
574
575
576
577
578
579
580
581
582
583
584
585
586
587
588
589
590
591
592
593
594
595
596
597
598
599
600
601
602
603
604
605
606
607
608
609
610
611
612
613
614
615
616
617
618
619
620
621
622
623
624
625
626
627
628
629
630
631
632
633
634
635
636
637
638
639
640
641
642
643
644
645
646
647
648
649
650
651
652
653
654
655
656
657
658
659
660
661
662
663
664
665
666
667
668
669
670
671
672
673
674
675
676
677
678
679
680
681
682
683
684
685
686
687
688
689
690
691
692
693
694
695
696
697
698
699
700
701
702
703
704
705
706
707
708
709
710
711
712
713
714
715
716
717
718
719
720
721
722
723
724
725
726
727
728
729
730
731
732
733
734
735
736
737
738
739
740
741
742
743
744
745
746
747
748
749
750
751
752
753
754
755
756
757
758
759
760
761
762
763
764
765
766
767
768
769
770
771
772
773
774
775
776
777
778
779
780
781
782
783
784
785
786
787
788
789
790
791
792
793
794
795
796
797
798
799
800
801
802
803
804
805
806
807
808
809
810
811
812
813
814
815
816
817
818
819
820
821
822
823
824
825
826
827
828
829
830
831
832
833
834
835
836
837
838
839
840
841
842
843
844
845
846
847
848
849
850
851
852
853
854
855
856
857
858
859
860
861
862
863
864
865
866
867
868
869
870
871
872
873
874
875
876
877
878
[
  {
    "question": "Mata na kuɓuta daga gorin mazansu saboda iya",
    "a": "dafa abinci",
    "b": "magana",
    "c": "kyauta",
    "d": "cin abinci",
    "answerKey": "a",
    "context": "A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.\n\nA wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.\n\nCikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Za a iya bayyana Tbi da cewa . ce",
    "a": "matattara",
    "b": "ma'aikata",
    "c": "mararraba",
    "d": "makaranta",
    "answerKey": "a",
    "context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa  ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da  ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe,  ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Me yaƙe-yaƙen arnan ya haifar?",
    "a": "Shirya kome bisa lalama",
    "b": "Cin mutane",
    "c": "Naɗa Razdan na Binuwai",
    "d": "Kashe hanyar ciniki.",

    "question": "A Ganɗoki na Walin Katsina A. Bello an nuna Ganɗoki ya yi faɗa har da",
    "a": "aljannu",
    "b": "mata",
    "c": "dabbobi",
    "d": "sarauniya",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Literature"
  },
  {
    "question": "Saƙar zuci na nufin:",
    "a": "\ntunan",
    "b": "zantuka",
    "c": "surkulle",
    "d": "zane-zane",
    "answerKey": "a",
    "context": "\"Ina cikin sakar zuci sai Gumuzu yajuyo gare ni ya ce,\"Umar, ga Abdulkarim ya roke ni arziki yana son ka. Son nan da yake maka ba wai ka zama bawansa ne ba.Yana so in ka dauka a ranka, ka ga za ka iya zama da shi ka zama ɗansa, gama ba shi da ɗa, ko ɗan dangi ma\nbabu a gare shi. Ni na yarda ku tafi tare da shi, yanzu yardarka ce kawai muke jira!\nBayan wannan, sai na ɗaga kai kawai ina duban nisan ƙasar su Adulkarim, kuma ina tunawa gyaturmata lara da rai ba ta ma san inda Allah ya shilla da ni ba.\n   A wurin sai duniyan nan ta taru ta yimini baƙi ƙirin ban san sa'ad da hawaye ya zubo mini ba. Da ganin haka sai Abdulkarim ya tambaye ni wai ko ba ni son sa ne? Ni kuwa na amsa masa ba haka ba ne, ba ni so ne in rabu da kasarmu. In na bi shi yaushe zan dawo gida? Shi kuma ya ce mini kowace shekara in zai zo lallai zai zo da ni domin in duba mutanen ƙasarnmu.\n   Nace, To, na yarda'. Don kada su ce na cika rashin kunya bayan kuwa da sun yabe ni. Bayan da aka gama wannan magana sarai na yarda, sai Gumuzu ya ce mini in koma gida. Da na tashi zan tafi sai Abdulkarim ya kawo kantu babba ya ba ni, game da waɗansu dabinai ƙeƙasassu waɗanda babu irinsu ga zaƙi.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Tun farko me ya habaka bauta a Sakkwato?",
    "a": "Kai gaisuwar bayi can",
    "b": "Wurin ya fi dacewa da bayi",
    "c": "An fi kanen bayi a can",
    "d": "Wurin ya fi kyawun noma",
    "answerKey": "a",
    "context": "Bayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n   Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "“Ita ko bante ta ƙetara sai ta haihu, In ka san kuɗi su ƙare a suna” Wannan tsakure na ‘Waƙar Zambon Ƙazama’ ta Mal. Aliyu Namangi, ta Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Da Da Na Yanzu, na D. Abdulkadir yana Magana ne a kan",
    "a": "masu gwanne",
    "b": "tsofaffi",
    "c": "mata karuwai",
    "d": "zawarawa",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Song"
  },
  {
    "question": "Yara masu laƙabi cindo an haife su ne",
    "a": "da yatsu shida",
    "b": "lokacin cin doya",
    "c": "da damina",
    "d": "ana ruwa",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "abokan gabarmu",
    "a": "Makiyanmu",
    "b": "Abokan taliyarrmu",
    "c": "Masoyanmu[Maryam Sa15]",
    "d": "Abokan aikinmu",
    "answerKey": "a",
    "context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n   Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n  Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Manufar na-gani-ina-so, ita ce bayyana",
    "a": "niyya",
    "b": "samun duniya",
    "c": "asali",
    "d": "wurin zama",
    "answerKey": "a",
    "context": "‘‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.\n\nYanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?\n\nGangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kaɗan!\n\nKada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.\n\nDuk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.\n\nHaƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Wanne ne bare dangane da jinsi?",
    "a": "Buraƙa",
    "b": "Hankaka",
    "c": "Cinnaka",
    "d": "Gauraka",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Grammar"
  },
  {
    "question": "‘Gaba da gabanta in ji Hausawa. Da su wa ko da\nme za ka danganta wannan?\n",
    "a": "Sarkin Borot da na Lantang",
    "b": "Ama da Turawa",
    "c": "Ibi da Muri",
    "d": "Jama'ar Gazum da Gyun",
    "answerKey": "a",
    "context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa  ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da  ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe,  ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Gamu na nufin...",
    "a": "yarda",
    "b": "rike",
    "c": "mance",
    "d": "kore",
    "answerKey": "a",
    "context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "A al’adance, wacce hanya ce aka fi amfani da ita wajen magance ciwo?",
    "a": "Jiƙo",
    "b": "Turare",
    "c": "Tauna",
    "d": "Surace",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Masu ilmin tarihi sun nuna cewa Musulunci ya zo kasar Hausa wajen karni na ...\n",
    "a": "sha ɗaya[Maryam Sa5]",
    "b": "sha biyar",
    "c": "sha tara",
    "d": "sha biyu",
    "answerKey": "a",
    "context": "\nShigowar Musulunci Kasar Hausa\n    Masu ilmin tarihi sun nuna cewa kafin Musulunci ya iso ƙasar Hausa sai da ya fara biyowa ta wasu sassa na ƙasashen Afirka ta Yamma tukuna. kamar Senegal da Mali, a wajen ƙarni na goma sha ɗaya. Amma kuma malaman addini kamar limamin Bauchi Alhaji Ahmadu Muhammad da Alhaji Nasiru Kabara na Kano sun nuna cewa Musulunci ya iso Afirka ta Yammna,musammart Agadas da Barno, sannan ya ƙaraso ƙasar Hausa tun a zamanin Sayyadina Mu'awiyya dan Safiyanu, wanda ya turo Uƙuba Ibn Nafi ya zo ya kawo Musulunci da litattafan addini Afrika ta Yamma. Shi dai Sayyadina Mu'awiyya ya yi zamani ne a ƙami\nIna 7.\n  Waɗansu malaman kuma sun nuna cewa Musulunci ya shigo Barno a zamanin sarautar Mai Dunama (1098-1150) wanda ya aiki wakilinsa Gujalo zuwa Makka wajen Halifa Abubakar Sadik (632-634) don ya karɓo saɗon Musulunci. Amma Gujalo ya tarar Halifa Abubakar ba shi da lafiya, har ma ya yi wafati, Gujalo bai sami saduwa da shi ba. Sai Sayyadina Umar ya hau Halifa (634-644), ya sadu da Gujalo, ya haɗa shí da manzonsa Amr bn Asi, ya ba shi Kur'ani mai girma da rawunna, da takobi, da garkuwoyi, da masu, da alkyabba iri-iri, da 'yan rakiya Larabawa ɗaruruwa don a kai wa Sarkin Barno. Da suka isa Barno sai suka shiga yaɗa addinin Musulunci da koyar da ilmi. Daga cikin Larabawan da suka biyo Gujalo, kimanin 300 suka bazu cikin kasar Hausa suka yaɗa Musulunci da koyar da ilmi.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Gyatumata na nufin",
    "a": "uwa",
    "b": "mai ɗaki",
    "c": "kwau",
    "d": "gwaggo",
    "answerKey": "a",
    "context": "\"Ina cikin sakar zuci sai Gumuzu yajuyo gare ni ya ce,\"Umar, ga Abdulkarim ya roke ni arziki yana son ka. Son nan da yake maka ba wai ka zama bawansa ne ba.Yana so in ka dauka a ranka, ka ga za ka iya zama da shi ka zama ɗansa, gama ba shi da ɗa, ko ɗan dangi ma\nbabu a gare shi. Ni na yarda ku tafi tare da shi, yanzu yardarka ce kawai muke jira!\nBayan wannan, sai na ɗaga kai kawai ina duban nisan ƙasar su Adulkarim, kuma ina tunawa gyaturmata lara da rai ba ta ma san inda Allah ya shilla da ni ba.\n   A wurin sai duniyan nan ta taru ta yimini baƙi ƙirin ban san sa'ad da hawaye ya zubo mini ba. Da ganin haka sai Abdulkarim ya tambaye ni wai ko ba ni son sa ne? Ni kuwa na amsa masa ba haka ba ne, ba ni so ne in rabu da kasarmu. In na bi shi yaushe zan dawo gida? Shi kuma ya ce mini kowace shekara in zai zo lallai zai zo da ni domin in duba mutanen ƙasarnmu.\n   Nace, To, na yarda'. Don kada su ce na cika rashin kunya bayan kuwa da sun yabe ni. Bayan da aka gama wannan magana sarai na yarda, sai Gumuzu ya ce mini in koma gida. Da na tashi zan tafi sai Abdulkarim ya kawo kantu babba ya ba ni, game da waɗansu dabinai ƙeƙasassu waɗanda babu irinsu ga zaƙi.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Akan kira ɗan da aka haifa bayan tagwaye",
    "a": "Gambo",
    "b": "Audi",
    "c": "Cindo",
    "d": "Damina",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Wace sarauta ce ta shafi kula da baitulmali?",
    "a": "Ma’aji",
    "b": "Sarkin fada",
    "c": "Sarkin gida",
    "d": "Waziri",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "‘‘Ja ya faɗo, ja ya ɗauka’’ Wane rukunin adabin baka wannan magana ta fito?",
    "a": "Maganganun azanci",
    "b": "Zuben baka",
    "c": "Salon magana",
    "d": "Waƙoƙin baka",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Oral literature"
  },
  {
    "question": " Me ya fi dacewa da bayyana Wase?\n",
    "a": "Mahaɗa[Maryam Sa3]",
    "b": "Kauye",
    "c": "Karkara",
    "d": "Maraba",
    "answerKey": "a",
    "context": "“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa  ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da  ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe,  ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Tsirar da Shaihu Umar ya yi shi kaɗai bayan hadari, ta ba da damar",
    "a": "ci gaban labarin",
    "b": "taƙaita labarin",
    "c": "gintse labarin",
    "d": "ƙayata labarin",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Literature"
  },
  {
    "question": "Wane ne ya shigar da Salihi cikin ƙungiyar asiri?",
    "a": "Kasa.",
    "b": "Monitansu.",
    "c": "Dahiru.",
    "d": "Malaminsu.",
    "answerKey": "a",
    "context": "A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.\n\nBayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.\n\nDa ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.\n\nGanin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Yaya Turawa za su dauki wanda ya gan su ya so\ngudu?",
    "a": "Makiyi",
    "b": "Matsoraci.",
    "c": "Mai zumudi.",
    "d": "Maras Ladabi.",
    "answerKey": "a",
    "context": "A shekara ta 1897 zamanin Sarkin Bida Abubakar, Turawa suka yi karon batta da Nufawa. Kafin nan, Turawa sun shekara uku cur suna godo da sarki su hadu da shi cikin aminci a wani wuri da ake kira Egbaji, yana kin zuwa. Har ma a wani lokaci sai da Turawan suka nada wani Muhammadu Makun a madadinsa. Duk da haka a cikin 1900 kusan a ce sarki biyu ke akwai a Bida, tsohon sarki da wanda Turawa suka nada.\n   Ana cikin haka, ran nan dai sai Gwamna Lugga ya aika wa Sarkin Bida da takarda, ya ce masa ya dai yi kokari ya zo ya sadu da shi a fadar Kogin Kaduna, kuma kada ya ii tsoron kome. Gwamna ya kara da cewa ba abin da za a yi masa, zai zo lafiya ya koma\nlafiya.\n   A wannan karon ma sai Sarkin Bida ya ki zuwa. Makun ne da 'yan rakiyarsa suka amsa kira, suka je wurin Gwamna Lugga. Saboda haka Turawa suka dauri aniyar zuwa Bida. Suka shaida wa jama'a muddin dai ba an taba su ba, babu fada. Kuma duk mutumin da suka ga don ganin su ya yi haramar gudu, za su dauke shi a mazaunin makiyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aika wa Sarki Abubakar da cewa kodayake dai Makun ne suka dauka kamar sarki, duk da haka idan shi\nAbubakar ya yarda suka sadu ko a Bida ne, ba zai wulakanta shi ba. Zai sa shi cikin jin dadi har abada.\nAmma duk a banza. Maimnakon ya tauso sai ya gudu ya tasar wa Lafai. Amma fa fitar kutsu ya yi, domin daga shi sai fadawa kamar shida ya bar Bida Aka yi irin abin nan wuji-wuji-ina-gabas, aka i xashe[Maryam Sa8]  manyan sarakunansa, aka yi wa wadansu iaur[Maryam Sa9] , aka kama na kamawa. Wadanda aka kama bayan sun wartsake sarai aka sake su. ",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "’Yan wasa mata nawa ne a Kukan Kurciya na M. B. Bambale?",
    "a": "Uku",
    "b": "Biyu",
    "c": "Huɗu",
    "d": "Biyar",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Theatre"
  },
  {
    "question": "Wanda shaƙuwar abota ta haɗa ku, shine",
    "a": "amini",
    "b": "shaƙiƙi",
    "c": "aboki",
    "d": "masoyi",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Me furen tumfafiya kan ƙara wa mutum?",
    "a": "Ƙwarinƙashi",
    "b": "Farin jini",
    "c": "Kwarjini",
    "d": "Jarumtaka",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Wane suna ya fi dacewa da wannan labarin?",
    "a": "‘Noma tushen arziƙi.’",
    "b": "‘Daidai ruwa daidai kurji.’",
    "c": "‘Da ruwan ciki ake jan na rijiya.’",
    "d": "‘kowa ya daka rawar wani …’",
    "answerKey": "a",
    "context": "Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: ɗaya ya yiwu an ci an ƙoshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.\n\nKullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.\n\nA al’adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ƙosai ko kunu. Wasu kuma, sukan ɗumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ɗanwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kuɓewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai “Daidai ruwa daidai ƙurji.”\n\nHar ila yau, ko da yake ba kowa yake da ƙarfin ɗora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami maƙwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira maƙwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ɗan’uwansa.\n\nA zamanin da, za a ga Bahaushe yana ƙoƙarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Kimanin Larabawa nawa suka biyo Gujalo zuwa Barno?",
    "a": "ɗari uku",
    "b": "ɗari biyar",
    "c": "ɗari biyu da shirin",
    "d": "ɗari uku da hamsin.",
    "answerKey": "a",
    "context": "\nShigowar Musulunci Kasar Hausa\n    Masu ilmin tarihi sun nuna cewa kafin Musulunci ya iso ƙasar Hausa sai da ya fara biyowa ta wasu sassa na ƙasashen Afirka ta Yamma tukuna. kamar Senegal da Mali, a wajen ƙarni na goma sha ɗaya. Amma kuma malaman addini kamar limamin Bauchi Alhaji Ahmadu Muhammad da Alhaji Nasiru Kabara na Kano sun nuna cewa Musulunci ya iso Afirka ta Yammna,musammart Agadas da Barno, sannan ya ƙaraso ƙasar Hausa tun a zamanin Sayyadina Mu'awiyya dan Safiyanu, wanda ya turo Uƙuba Ibn Nafi ya zo ya kawo Musulunci da litattafan addini Afrika ta Yamma. Shi dai Sayyadina Mu'awiyya ya yi zamani ne a ƙami\nIna 7.\n  Waɗansu malaman kuma sun nuna cewa Musulunci ya shigo Barno a zamanin sarautar Mai Dunama (1098-1150) wanda ya aiki wakilinsa Gujalo zuwa Makka wajen Halifa Abubakar Sadik (632-634) don ya karɓo saɗon Musulunci. Amma Gujalo ya tarar Halifa Abubakar ba shi da lafiya, har ma ya yi wafati, Gujalo bai sami saduwa da shi ba. Sai Sayyadina Umar ya hau Halifa (634-644), ya sadu da Gujalo, ya haɗa shí da manzonsa Amr bn Asi, ya ba shi Kur'ani mai girma da rawunna, da takobi, da garkuwoyi, da masu, da alkyabba iri-iri, da 'yan rakiya Larabawa ɗaruruwa don a kai wa Sarkin Barno. Da suka isa Barno sai suka shiga yaɗa addinin Musulunci da koyar da ilmi. Daga cikin Larabawan da suka biyo Gujalo, kimanin 300 suka bazu cikin kasar Hausa suka yaɗa Musulunci da koyar da ilmi.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Shiga-ka-fito wajen neman aure ta fi alaƙa da",
    "a": "kashe kuɗi",
    "b": "gaishe-gaishe",
    "c": "karakaina",
    "d": "kamun ƙafa",
    "answerKey": "a",
    "context": "‘‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.\n\nYanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?\n\nGangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kaɗan!\n\nKada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.\n\nDuk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.\n\nHaƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Tsuntsaye masu farautar nama da cinsa, suna da",
    "a": "baki mai karfi da kaifi, kafafuwa karfafa\nda kumba zako-zako",
    "b": "baki mai kaifi da karfi.",
    "c": "saurin tashin da baki mai tsawo da gwabi.",
    "d": "dogon wuya da baki mai karfi da kumba.",
    "answerKey": "a",
    "context": "Tsuntsaye wadanda ke farautar nama suna da halitta daidai wadda za ta dace da wannan aiki. Ga baki mai[Maryam Sa25] karfi da kaifi ya lankwasa kamar kugiya. Da shi suke kekketa nama. Ga su da kafa mai karfi da kumba zako-zako. In sun kawo sura, da su su ke fyauce[Maryam Sa26]  abin da suka farauta, su rike, su yi sama da shi. In za su ci, sai su kakkafa kumbobinsu ciki, su rike shi kam.\n  Shaho yana da saurin tafiya. Akwai wasu iri, in sun ga wani tsuntsu yana tashi sai su bi, kome saurin tashinsa, sai sun ishe sun buge. Su irin wadannan, mutane sun dade suna kiwon su domin farauta. In za a farauta, sai ka dauki shahonka a kafada, an daure shi  da sarka, an yi masa lullubi. In ka ga ko hasbiya tana tashi, sai ka bude kan shahonka ka sake shi, ya buge\nmaka.\nWannan irin farauta ta shahara a kasashen su Farisa da Hindu. Da, hara Turai an yi, amma yanzu an daina.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Da zarar abokin[Maryam Sa22]  gabar bauna ya kai kasa, ba wata[Maryam Sa23] -wata sai ta sa",
    "a": "tsinin kahonta ta tsire.",
    "b": "daginta ta soke.",
    "c": "tsininta ta tsire.",
    "d": "tsawonta ta tsire.",
    "answerKey": "a",
    "context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n   Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n  Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n   Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n  In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n  Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n  In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18]  maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n  Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n  In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Malam nomau mutumin wane gari ne?",
    "a": "Kauyen Wudil.",
    "b": "Birnin Damagaram.",
    "c": "Birnin Katsina.",
    "d": "Bodinga.",
    "answerKey": "a",
    "context": "Yau Jumma'a Malam Nomau za shi cin kasuwa Wudil. Kafin ya tafi ya dauki wandonsa mai kamun kafa, ya bude ya sa shi ya zuba babbar rigarsa bullan da hular dara da falmaran, da takalmi sani tsalle, da 'yar ciki, da rawani mubarashi ya rataye shi. Kuma yana saye da wando buje da 'yar shara, da hula habar kada da takalmin fade.\nDa isowarsa kofar gari sai ya raba gindin wata tsamiya ya fito da kayan nan nasa na cikin wando ya caba ado bayan ya wanke jikinsa. Ya kuma zuba turare dan-goma, ya bara goro marsa ya cika bakinsa ya yi kumurya. Ya kunshe tsofaffin kayansa buje, ya make a hammatarsa ya shiga gari ya kai gidan abokinsa ya ajiye. Matar abokinsa ta ba shi farau-farau ya sha. Daga nan sai ya tafi cin kasuwa.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Meya sa Turawa suke neman Sarki ya sadu da\nsu?",
    "a": "Don su yi aminci.",
    "b": "Don su kara masa girma.",
    "c": "Don su rage masa girma.",
    "d": "Don ya ba su wajen noma.",
    "answerKey": "a",
    "context": "A shekara ta 1897 zamanin Sarkin Bida Abubakar, Turawa suka yi karon batta da Nufawa. Kafin nan, Turawa sun shekara uku cur suna godo da sarki su hadu da shi cikin aminci a wani wuri da ake kira Egbaji, yana kin zuwa. Har ma a wani lokaci sai da Turawan suka nada wani Muhammadu Makun a madadinsa. Duk da haka a cikin 1900 kusan a ce sarki biyu ke akwai a Bida, tsohon sarki da wanda Turawa suka nada.\n   Ana cikin haka, ran nan dai sai Gwamna Lugga ya aika wa Sarkin Bida da takarda, ya ce masa ya dai yi kokari ya zo ya sadu da shi a fadar Kogin Kaduna, kuma kada ya ii tsoron kome. Gwamna ya kara da cewa ba abin da za a yi masa, zai zo lafiya ya koma\nlafiya.\n   A wannan karon ma sai Sarkin Bida ya ki zuwa. Makun ne da 'yan rakiyarsa suka amsa kira, suka je wurin Gwamna Lugga. Saboda haka Turawa suka dauri aniyar zuwa Bida. Suka shaida wa jama'a muddin dai ba an taba su ba, babu fada. Kuma duk mutumin da suka ga don ganin su ya yi haramar gudu, za su dauke shi a mazaunin makiyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aika wa Sarki Abubakar da cewa kodayake dai Makun ne suka dauka kamar sarki, duk da haka idan shi\nAbubakar ya yarda suka sadu ko a Bida ne, ba zai wulakanta shi ba. Zai sa shi cikin jin dadi har abada.\nAmma duk a banza. Maimnakon ya tauso sai ya gudu ya tasar wa Lafai. Amma fa fitar kutsu ya yi, domin daga shi sai fadawa kamar shida ya bar Bida Aka yi irin abin nan wuji-wuji-ina-gabas, aka i xashe[Maryam Sa8]  manyan sarakunansa, aka yi wa wadansu iaur[Maryam Sa9] , aka kama na kamawa. Wadanda aka kama bayan sun wartsake sarai aka sake su. ",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Wace sana’a ce aka fi sanin mata zalla da yi?",
    "a": "Kaɗi",
    "b": "Saƙar tabarma",
    "c": "Ginin tukwane",
    "d": "Ɗinki",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Shaho yana da saurin tafiya.' Wannan jumlan nufin shaho na da",
    "a": "saurin tashi.",
    "b": "saurin tafiya bisa doron kasa.",
    "c": "saurin tafiya a kasa idan ya ga nama",
    "d": "saurin tafiya, sama da kasa.",
    "answerKey": "a",
    "context": "Tsuntsaye wadanda ke farautar nama suna da halitta daidai wadda za ta dace da wannan aiki. Ga baki mai[Maryam Sa25] karfi da kaifi ya lankwasa kamar kugiya. Da shi suke kekketa nama. Ga su da kafa mai karfi da kumba zako-zako. In sun kawo sura, da su su ke fyauce[Maryam Sa26]  abin da suka farauta, su rike, su yi sama da shi. In za su ci, sai su kakkafa kumbobinsu ciki, su rike shi kam.\n  Shaho yana da saurin tafiya. Akwai wasu iri, in sun ga wani tsuntsu yana tashi sai su bi, kome saurin tashinsa, sai sun ishe sun buge. Su irin wadannan, mutane sun dade suna kiwon su domin farauta. In za a farauta, sai ka dauki shahonka a kafada, an daure shi  da sarka, an yi masa lullubi. In ka ga ko hasbiya tana tashi, sai ka bude kan shahonka ka sake shi, ya buge\nmaka.\nWannan irin farauta ta shahara a kasashen su Farisa da Hindu. Da, hara Turai an yi, amma yanzu an daina.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "‘‘ƙulun-ƙulu-fita.’’",
    "a": "Gauta",
    "b": "Baba",
    "c": "Kanwa",
    "d": "Gishiri",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Oral literature"
  },
  {
    "question": "Lokaci Na Yanzu II shi ne mai manunin lokaci",
    "a": "-ke",
    "b": "za",
    "c": "-na",
    "d": "-kan",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Grammar"
  },
  {
    "question": "Me ake nufi da gwama nunfashi a labarin?",
    "a": "Ka-ce-na-ce.",
    "b": "Rayuwa.",
    "c": "Ƙwazo.",
    "d": "Saki-na-dafe.",
    "answerKey": "a",
    "context": "Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: ɗaya ya yiwu an ci an ƙoshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.\n\nKullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.\n\nA al’adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ƙosai ko kunu. Wasu kuma, sukan ɗumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ɗanwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kuɓewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai “Daidai ruwa daidai ƙurji.”\n\nHar ila yau, ko da yake ba kowa yake da ƙarfin ɗora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami maƙwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira maƙwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ɗan’uwansa.\n\nA zamanin da, za a ga Bahaushe yana ƙoƙarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Makoɗi kayan aiki ne na",
    "a": "ƙira",
    "b": "jima",
    "c": "sassaƙa",
    "d": "wanzanci",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Sayyadina Mu'awiyya ya yi zamani a ƙami na ...\n",
    "a": "7",
    "b": "18",
    "c": "17",
    "d": "27",
    "answerKey": "a",
    "context": "\nShigowar Musulunci Kasar Hausa\n    Masu ilmin tarihi sun nuna cewa kafin Musulunci ya iso ƙasar Hausa sai da ya fara biyowa ta wasu sassa na ƙasashen Afirka ta Yamma tukuna. kamar Senegal da Mali, a wajen ƙarni na goma sha ɗaya. Amma kuma malaman addini kamar limamin Bauchi Alhaji Ahmadu Muhammad da Alhaji Nasiru Kabara na Kano sun nuna cewa Musulunci ya iso Afirka ta Yammna,musammart Agadas da Barno, sannan ya ƙaraso ƙasar Hausa tun a zamanin Sayyadina Mu'awiyya dan Safiyanu, wanda ya turo Uƙuba Ibn Nafi ya zo ya kawo Musulunci da litattafan addini Afrika ta Yamma. Shi dai Sayyadina Mu'awiyya ya yi zamani ne a ƙami\nIna 7.\n  Waɗansu malaman kuma sun nuna cewa Musulunci ya shigo Barno a zamanin sarautar Mai Dunama (1098-1150) wanda ya aiki wakilinsa Gujalo zuwa Makka wajen Halifa Abubakar Sadik (632-634) don ya karɓo saɗon Musulunci. Amma Gujalo ya tarar Halifa Abubakar ba shi da lafiya, har ma ya yi wafati, Gujalo bai sami saduwa da shi ba. Sai Sayyadina Umar ya hau Halifa (634-644), ya sadu da Gujalo, ya haɗa shí da manzonsa Amr bn Asi, ya ba shi Kur'ani mai girma da rawunna, da takobi, da garkuwoyi, da masu, da alkyabba iri-iri, da 'yan rakiya Larabawa ɗaruruwa don a kai wa Sarkin Barno. Da suka isa Barno sai suka shiga yaɗa addinin Musulunci da koyar da ilmi. Daga cikin Larabawan da suka biyo Gujalo, kimanin 300 suka bazu cikin kasar Hausa suka yaɗa Musulunci da koyar da ilmi.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Labarin kura da akuya da harawa yana cikin nau’in labari na",
    "a": "almara",
    "b": "kacici-kacici",
    "c": "ƙissa",
    "d": "tatsuniya",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Oral literature"
  },
  {
    "question": "‘Ya zama musu alaƙaƙai, ko wane juyin suka yi na su halaka shi, shi ke sama, sai ka ce hancin gauta.’ Wane irin salo aka yi amfani da shi a wannan tsakure na Ganɗoki na Walin Katsina A. Bello?",
    "a": "Kamantawa",
    "b": "Mutuntarwa",
    "c": "Dabbantawa",
    "d": "Ƙarangiya",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Literature"
  },
  {
    "question": "A labarin, nau’o’in abinci nawa aka lissafa?",
    "a": "Tara",
    "b": "Bakwai",
    "c": "Takwas",
    "d": "Shida",
    "answerKey": "a",
    "context": "A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.\n\nA wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.\n\nCikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Su wa Makau ya kira jakkai a wasan Shaihu Umar na U. Ladan Da D. Lyndersay?",
    "a": "Ƙwatau da Sarkin Zagi",
    "b": "Ƙwatau da Wawan Sarki",
    "c": "Shantali da Ƙwatau",
    "d": "Sarkin Zagi da Wawan Sarki",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Theatre"
  },
  {
    "question": "Su wa suka fi yin waƙoƙin talla?",
    "a": "’Yan mata",
    "b": "’Yan maza",
    "c": "’Yan galura",
    "d": "’Yan yara",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Oral literature"
  },
  {
    "question": "Yaushe manemin yarinya ke zuwa gayar da iyaye da kakanninta?",
    "a": "Bayan sa rana",
    "b": "Kafin baiko",
    "c": "Da soma ganin ta",
    "d": "Da an yi biki",
    "answerKey": "a",
    "context": "‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.\n\nYanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?\n\nGangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kaɗan!\n\nKada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.\n\nDuk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.\n\nHaƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Fadojin kuda su ne",
    "a": "juji, mahauta, mushe da gyambo",
    "b": "kwata, bola, mushe da gyambo.",
    "c": "kwata, bola, mushe da tuwo,",
    "d": "madafi, mahauta da juji.",
    "answerKey": "a",
    "context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n   Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n  Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Wa ya taimaki Katsinawa a kan Kwararafawa?",
    "a": "Danmasani.",
    "b": "Waziri.",
    "c": "Sarki.",
    "d": "Daule",
    "answerKey": "a",
    "context": "A kwanakin Sarkin Katsina Jan-Hazo, Kwararrafawa suka je Katsina. Sarkinsu ya sauka yammacin gari a babbar ruga, wazirinsa kuma a gabashin gari. Sarkin ya kama mashinsa ya girgiza shi ya jefa cikin gari, ya fada tsohuwar kasuwa kusa da kududdufin Taukin Daule, sai wuta ta kama gun. Daga nan sarakunan Katsina suka taru wajen Sarki Jan-Hazo, suka yi kus- kus haka suka gamu a kan su fita su bar garin, mai tsira ya tsira, mai mutuwa ya mutu. Sai suka aika wa Malam Danmasani. Shi kuwa ya ce kada su fita, za su ga abin da Allah zai yi da Kwararrafawa. Ya dukufa rokon Ubangiji bisa wannan lamari.\n \nSai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, amma dokin ya shure shi a kan cibiya da dare ya fadi matacce. Da aka ba wazirinsa labarin abin da ya faru, sai nan da nan shi ma ya hau dokinsa, dokin ya ka da shi wuyansa ya karye, ya mutu. A cikin daren nan kuma manya-manyan sarakunansu bakwai suka ce ga garinku. Sai niyyar Kwararrafawa ta yaki ta wargaje, suka bar wajen. Daga nan Sarkin Katsina da kansa ya tafi wajen Danmasani ya durkusa ya yi masa godiya tare da goma na arziki.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Babbar fa’idar cin abinci tare, ita ce",
    "a": "sada zumunci tsakanin mutane",
    "b": "yalwar abinci daban-daban",
    "c": "sa mata su ƙara himma",
    "d": "wani zai yi santi da abincin wani",
    "answerKey": "a",
    "context": "A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.\n\nA wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.\n\nCikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Wace hanya ce ake bi domin shiga harkar bori?",
    "a": "Girka",
    "b": "Garaya",
    "c": "Addu’a",
    "d": "Shaushawa",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Jigon waƙar ‘‘Mu Sha Falala’’ ta Sarkin Zazzau Aliyu Ɗansidi a Waƙoƙin Hausa, shi ne",
    "a": "faɗakarwa",
    "b": "kasuwanci",
    "c": "yabo\n",
    "d": "siyasa",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Song"
  },
  {
    "question": "Tuddai nawa na neman aure aka ambata?",
    "a": "Bakwai",
    "b": "Biyar",
    "c": "Shida",
    "d": "Huɗu",
    "answerKey": "a",
    "context": "‘‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.\n\nYanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?\n\nGangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar. Ina, ko kaɗan!\n\nKada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.\n\nDuk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi. I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.\n\nHaƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Kekasa kasa[Maryam Sa7]  na nufin ...",
    "a": "ki",
    "b": "ji",
    "c": "kyankyasa kasa",
    "d": "tattaka kasa",
    "answerKey": "a",
    "context": "Bayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n   Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Mene ne mabuɗin jumla?",
    "a": "Yankin suna",
    "b": "Yankin bayanau",
    "c": "Yankin aikatau",
    "d": "Yankin karɓau",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Grammar"
  },
  {
    "question": "A labarin, akan yi ɗan wake da",
    "a": "rana",
    "b": "safe",
    "c": "almuru",
    "d": "asuba",
    "answerKey": "a",
    "context": "Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: ɗaya ya yiwu an ci an ƙoshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.\n\nKullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.\n\nA al’adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ƙosai ko kunu. Wasu kuma, sukan ɗumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ɗanwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kuɓewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai “Daidai ruwa daidai ƙurji.”\n\nHar ila yau, ko da yake ba kowa yake da ƙarfin ɗora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami maƙwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira maƙwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ɗan’uwansa.\n\nA zamanin da, za a ga Bahaushe yana ƙoƙarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Me ke sanya bayi karar iyayen gijinsu?",
    "a": "Neman 'yanci",
    "b": "Butulci.",
    "c": "Neman rigima",
    "d": "Takala",
    "answerKey": "a",
    "context": "Bayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n   Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Barunje shi ne",
    "a": "mahauci",
    "b": "malami",
    "c": "maharbi",
    "d": "masaƙi",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "Mene ne jigon Jatau Na Kyallu na S. Maƙarfi?",
    "a": "Auren karuwa",
    "b": "Butulcin mata",
    "c": "Neman haihuwa",
    "d": "Neman karuwa",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Theatre"
  },
  {
    "question": "Kuda ne ke kawo cutar",
    "a": "atuni, gudawa da ciwon ciki.",
    "b": "ciwon baya da ciki.",
    "c": "ciwon kai da gudawa.",
    "d": "ciwon kazuwa, gudawada atuni.",
    "answerKey": "a",
    "context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n   Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n  Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Wanda ya fi sanin halin bauna shi ne",
    "a": "babban maharbi.",
    "b": "babban direba[Maryam Sa20] .",
    "c": "Mal amin dawa.",
    "d": "sarkin baka.",
    "answerKey": "a",
    "context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n   Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n  Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n   Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n  In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n  Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n  In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18]  maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n  Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n  In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Marubucin Shaihu Umar ya yi amfani da salon harshe mai",
    "a": "ban tausayi",
    "b": "kaushi",
    "c": "ƙarangiya",
    "d": "ban haushi",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Literature"
  },
  {
    "question": "Mutumin da ake haɗuwa, a ci abinci gidansa, yana matsayin",
    "a": "shugaba",
    "b": "wakili",
    "c": "malami",
    "d": "hakimi",
    "answerKey": "a",
    "context": "A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.\n\nA wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.\n\nCikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "‘‘Wane ne ya ce da kai babu bashi tsakaninmu da kai! Ina gidana na bakin kasuwa wanda na gada daga wurin ubanmu ?’’\nA ina ake wannan magana a Jatau Na Kyallu na S. Maƙarfi?",
    "a": "A kotu",
    "b": "A ɗakin Kyallu",
    "c": "A ɗakin Uwargida",
    "d": "A tasha",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Theatre"
  },
  {
    "question": "Wannan alamar (–), ita aka fi sani da",
    "a": "karan ɗori",
    "b": "ruwa biyu",
    "c": "waƙafi",
    "d": "ɗebewa",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Grammar"
  },
  {
    "question": "Bauna na banke abokan gaba da",
    "a": "tushen kahoninta.",
    "b": "gangar jikinta.",
    "c": "wuyanla.",
    "d": "tsinin harshenta.",
    "answerKey": "a",
    "context": "BAUNA\nBauna saniya ce, sai dai ita ta ki yarda da dan Adam. Duk abin da ke ga saniya, to, 6auna tana da shi, ta fuskar halitta ba hali ba.\n   Bauna tana da fada kwarai, ta fi duk namun daji da ka sani sababi. Amma in ka fada garkensu a dawa ba za su taba ka ba. Dabbobi duk, in dai ba wuri ya kure ba, in sun ga mutum sun fi so su gudu.\n  Yana da ban sha'awa ka ga bauna na gudu cikin dawa. Ba za ka ga tana rangaji ba irin na saniya, wadda ta koyi ragwacin \"yan birni.\n   Ka san ba abin dariya kamar ka ga saniya na gudu. Amma bauna, ko da yake katuwa ce, in ka ga tana tsalle sai ka ce barewa. Ko da muka ce 6auna ba ta da jan fada, in ta yi tsanmani fad'a ya kawo ka sai ta tsaya a buga.\n  In kuwa har ka rigaya ka yi mata rauni, abu ya baci, sai ka san in da ka shiga.\n  Kowane babban maharbi zai iya ba ka labarin karon sa da bauna. \n  In kana bin sawun bauna, ta kuwa gane haka, sai ta yi maza la bace[Maryam Sa18]  maka, ta zago ta fito maka ta baya tanan sanda, sa annan ta bude baki. Kafin ka waiwaya, ka isa lahira!\nBa wata dabba mai yin haka sai bauna. Mafitarkan kawai in ka sani dama ka hau itace. Ko sa'annan ma, in itacen ba girma gare shi ba, sai takai masa karo, ya\nkarye.\n  Kahon bauna ba kamar na saniya ba ne. Nata kaurara ne, tushensu har ya rufe goshinta. Ba su da Lwaso[Maryam Sa19] kwarai, tsininsu ya lankwasa kamar zai sake tabo kwakwal war kanta.\n  In bauna ta kai sura sai ta duka da kai. Saboda haka sai kahonin su zama kamar garkuwa ga kanta. Ko maharbi ya harbi kan, ko da bindiga ne balle kibiya, in ya sami garkuwar ba zai cuce ta ba. Tushen nan mai kauri na kahonta da shi take banke abokin fada. In ya fadi, ta sa wajen tsinin ta tsire shi, ta jefa sama da taimakon kakkarfan wuyan nan nata. Bauna, kin ki duban raini!\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Wane ne tauraron labarin?",
    "a": "Salihi.",
    "b": "Mahaifin Salihi.",
    "c": "Kasa.",
    "d": "Mahaifiyar Salihi.",
    "answerKey": "a",
    "context": "A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.\n\nBayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.\n\nDa ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.\n\nGanin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "A ina yara mata suke waƙe-waƙensu na gaɗa?",
    "a": "Dandali",
    "b": "Gidan tsohuwa",
    "c": "Gidan amarya",
    "d": "Zaure",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Oral literature"
  },
  {
    "question": "Abubuwa nawa ne kuda ke yi dan yana ci mana\nabinci?",
    "a": "Biyu",
    "b": "Tara",
    "c": "Biyar",
    "d": "Daya",
    "answerKey": "a",
    "context": "Kudan gida na daya daga cikin abokan gabarmu. manya masu raba cuta ga 'ya Adam. Shi ke kawo su, atuni', da ciwon gudawa da sauran irinsu.\n   Amma shi kuda ba ya cizon mu kamar sauro da Isando. Hanyar da ya ke bi ya yi nasa mugun aiki ba daya ba ce da tasu. Su, suna tsotso kwayoyin cuta daga Cikin jini ne, su je su soki mai lafiya su dura masa. Amma bakin kuda ba a yi shi don ya yi cizo ba. Kuda ba ya iya huda fatar mutum, ba ya ma iya huda fatar kome, ko yana so. Harshensa da bakinsa duka taushi\ngare su.\nTsaya ka ji kazantar kuda. Ka san lalle, ko ba don cuta ba, kuda abin kyama ne. Wajibi ne kuma mu yi iyakar kokarinmu mu rabu da shi.\nBa abin da kuda ke so kamar ya ci luroson (najasar) dan Adam. In ya samu najasa, ya duka da ci, sai ka ce ka samu taliya. Kun san kuwa, in mutum ba shi da lafiya sau da yawa akan sami kwayoyin cuta a cikin najarsa.\nKai duk dai wurin kazanta, Mahauta ne, juji ne, wurin mushe ne, wurin gyambo ne duka dai nan ne fadar kuda.\n In sun ci sun taso, sai su yi face-face da kazantar har da kwayoyin cutar da ke ciki.\nDa ma kafafuwansu da ikinsu gashi gare Su, duk kuwa madauka dauda ne.\n \nDaga nan sai su zo su sauka kan abincinmu. \nKan san galibi, abincinmu wanda suka fi so shi ne kilishi, tsire, nono, sukari da su alewa. Kaga wadannan, in an saya ba a sake dafa su. saboda haka muna cin kazanta da yawa daga gare su.\n  Ban da wannan ma, in suna cin abincinmu, sukan rika amai bisansa suna tashi. Kazanta bisa kazanta! Ina ka ga lafiya?\n",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "Ɗanmaraya Jos ya na amfani ne da",
    "a": "kuntigi",
    "b": "gurmi",
    "c": "garaya",
    "d": "molo",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Culture"
  },
  {
    "question": "‘Wa ya ce ba ni ba! Wa ya yi ni, wa Yai kamata! Wa kuma zai kama bawa fiye da wanda zan kama!’ Wa ya yi wannan kirari a cikin Shaihu Umar na U. Ladan da D. Lyndersay?",
    "a": "Ƙwatau",
    "b": "Makau",
    "c": "Buhari",
    "d": "Shaihu",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Theatre"
  },
  {
    "question": "Wane mataki Turawa suka dauka bayan bijirewar\nSarki?",
    "a": "Nada wani[Maryam Sa10]  daban.",
    "b": "Gargadin sa.",
    "c": "Tsare shi.",
    "d": "Rarrashin sa.",
    "answerKey": "a",
    "context": "A shekara ta 1897 zamanin Sarkin Bida Abubakar, Turawa suka yi karon batta da Nufawa. Kafin nan, Turawa sun shekara uku cur suna godo da sarki su hadu da shi cikin aminci a wani wuri da ake kira Egbaji, yana kin zuwa. Har ma a wani lokaci sai da Turawan suka nada wani Muhammadu Makun a madadinsa. Duk da haka a cikin 1900 kusan a ce sarki biyu ke akwai a Bida, tsohon sarki da wanda Turawa suka nada.\n   Ana cikin haka, ran nan dai sai Gwamna Lugga ya aika wa Sarkin Bida da takarda, ya ce masa ya dai yi kokari ya zo ya sadu da shi a fadar Kogin Kaduna, kuma kada ya ii tsoron kome. Gwamna ya kara da cewa ba abin da za a yi masa, zai zo lafiya ya koma\nlafiya.\n   A wannan karon ma sai Sarkin Bida ya ki zuwa. Makun ne da 'yan rakiyarsa suka amsa kira, suka je wurin Gwamna Lugga. Saboda haka Turawa suka dauri aniyar zuwa Bida. Suka shaida wa jama'a muddin dai ba an taba su ba, babu fada. Kuma duk mutumin da suka ga don ganin su ya yi haramar gudu, za su dauke shi a mazaunin makiyinsu. Har ma Gwamna Lugga ya aika wa Sarki Abubakar da cewa kodayake dai Makun ne suka dauka kamar sarki, duk da haka idan shi\nAbubakar ya yarda suka sadu ko a Bida ne, ba zai wulakanta shi ba. Zai sa shi cikin jin dadi har abada.\nAmma duk a banza. Maimnakon ya tauso sai ya gudu ya tasar wa Lafai. Amma fa fitar kutsu ya yi, domin daga shi sai fadawa kamar shida ya bar Bida Aka yi irin abin nan wuji-wuji-ina-gabas, aka i xashe[Maryam Sa8]  manyan sarakunansa, aka yi wa wadansu iaur[Maryam Sa9] , aka kama na kamawa. Wadanda aka kama bayan sun wartsake sarai aka sake su. ",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.",
    "category": "Reading comprehension"
  },
  {
    "question": "labarin ‘Kowa Ya Dogara Ga Allah, Kada Ya Ji Tsoron Mahassada, Balle Ƙeta’ na cikin Magana Jari Ce na III na A. Imam, ya amsa sunansa ganin yadda",
    "a": "aka halaka Waziri",
    "b": "Sarkin Ƙaraya ya cika umarnin Sarkin Sudan",
    "c": "aka yi shagalin sarautar Abdun Ugu",
    "d": "Abdun Ugu ya ƙetare makircin Waziri",
    "answerKey": "a",
    "context": "",
    "grade": "SS3",
    "preamble": "",
    "category": "Literature"
  },
  {
    "question": "Buje' cikin wannan labarin na Iá tin",
    "a": "wando masunta.",
    "b": "wando dan-itori.",
    "c": "wando 'yan sanda.",
    "d": "fankacecen wando mai mazagi",

  }
]