[ { "question": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.\n\nMata na kuɓuta daga gorin mazansu saboda iya\n\nA karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.\n\nA wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.\n\nCikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi. Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.", "mc1_targets": { "choices": [ "dafa abinci", "magana", "kyauta", "cin abinci" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "dafa abinci", "magana", "kyauta", "cin abinci" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.\n\nZa a iya bayyana Tbi da cewa . ce\n\n“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe, ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"", "mc1_targets": { "choices": [ "matattara", "ma'aikata", "mararraba", "makaranta" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "matattara", "ma'aikata", "mararraba", "makaranta" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.\n\nMe yaƙe-yaƙen arnan ya haifar?\n\n“Tun lokacin da ƙasar nan hannun Turawan kamfani, suna da wani kantinsu da kome nasu a Ibi[Maryam Sa1] . Daga nan ne bayan gwamnati ta amshi mulki daga hannun kamfanin aka sami damar isa ƙasar Muri. Razdan na Binuwai Mista Hewby ya yi iyakacin ƙoƙarinsa da ya ƙaru da labarun da ƙasar take ciki.\nAman da ke sashen Arewa na ƙasar an ce Suna cin mutane, kuma ba su san kome ba na game da sha'anin a shirya kome bisa lalama. Su ne ma saboda yaƙe- yaƙensu suka kashe hanyar ciniki mai zuwa Bauci. Manyan hanyoyin ciniki uku, ɗaya daga inda ake kawo gishiri, wato Awe, ɗaya kuma daga wajen Kamaru, ɗaya kuma daga Gashaka, dukansu sun haɗu a Wase ne. Ba dai irin ƙoƙarin da Fulani ma ba su yi ba don su sa hanyar nana ta zauna yadda ya kamata, amma abin ya ci tura. Hasali ma dai a cikin 1903 ƙasar Wase sai da ta kai aka raba ta da jin ko taɗ’in mutanen Yalwa. Har ma aka yi wa waɗansu fatake shida fashi, aka kashe su baki ɗaya. Dalilin haka ne Gwamna Lugga a cikin 1904 ya tura soja suka tasar wa Bauci don a buɗe hanya, kowa ya saki jikinsa.\nAka dai ciwo kanarnan nan da suka addabi mutane. Har ma cikin lokaci ƙanƙane suka biya tarar da aka yi masu, suka fanshi kansu da jaka huɗu da rabi. Irin dogon bayanin da aka yi wa arnan nan, shi ya sa ba su sake ta da fitina ba. Aka nuna masu zamani ya juya, ba kamar irin cin da Fulani suka yi wa mutane su Turawa ke yi ba. Kuma fitar da wadansu shugabanninsu, da\nhoron masu tsananin laiti, duk yana cikin abubuwan da suka sa suka yi taushi. Aka tuɓe Sarkin Borot da na Lantang- Jama'ar da ake kira Gazum da Gyun kuma shuka ce suna so a fitar da sarkinsu, domin shi ne ya jawo masu wannan masila. Aka litar da Vondup sarkin nasu.\"", "mc1_targets": { "choices": [ "Shirya kome bisa lalama", "Cin mutane", "Naɗa Razdan na Binuwai", "Kashe hanyar ciniki." ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "Shirya kome bisa lalama", "Cin mutane", "Naɗa Razdan na Binuwai", "Kashe hanyar ciniki." ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "A Ganɗoki na Walin Katsina A. Bello an nuna Ganɗoki ya yi faɗa har da", "mc1_targets": { "choices": [ "aljannu", "mata", "dabbobi", "sarauniya" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "aljannu", "mata", "dabbobi", "sarauniya" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.\n\nSaƙar zuci na nufin:\n\n\"Ina cikin sakar zuci sai Gumuzu yajuyo gare ni ya ce,\"Umar, ga Abdulkarim ya roke ni arziki yana son ka. Son nan da yake maka ba wai ka zama bawansa ne ba.Yana so in ka dauka a ranka, ka ga za ka iya zama da shi ka zama ɗansa, gama ba shi da ɗa, ko ɗan dangi ma\nbabu a gare shi. Ni na yarda ku tafi tare da shi, yanzu yardarka ce kawai muke jira!\nBayan wannan, sai na ɗaga kai kawai ina duban nisan ƙasar su Adulkarim, kuma ina tunawa gyaturmata lara da rai ba ta ma san inda Allah ya shilla da ni ba.\n A wurin sai duniyan nan ta taru ta yimini baƙi ƙirin ban san sa'ad da hawaye ya zubo mini ba. Da ganin haka sai Abdulkarim ya tambaye ni wai ko ba ni son sa ne? Ni kuwa na amsa masa ba haka ba ne, ba ni so ne in rabu da kasarmu. In na bi shi yaushe zan dawo gida? Shi kuma ya ce mini kowace shekara in zai zo lallai zai zo da ni domin in duba mutanen ƙasarnmu.\n Nace, To, na yarda'. Don kada su ce na cika rashin kunya bayan kuwa da sun yabe ni. Bayan da aka gama wannan magana sarai na yarda, sai Gumuzu ya ce mini in koma gida. Da na tashi zan tafi sai Abdulkarim ya kawo kantu babba ya ba ni, game da waɗansu dabinai ƙeƙasassu waɗanda babu irinsu ga zaƙi.\n", "mc1_targets": { "choices": [ "\ntunan", "zantuka", "surkulle", "zane-zane" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "\ntunan", "zantuka", "surkulle", "zane-zane" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.\n\nTun farko me ya habaka bauta a Sakkwato?\n\nBayan shekara biyu da lakwame Sakkwato sai al'amarin bauta ya yi sauki. Bayi suka sami damar kai kara dakin shari'a idan suna bukatar su fanshi kansu. Kuma idan har mutum yana da bawa, bawan nan ya nuna yana so a 'yanta shi, amma ubangijinsa ya kekasa Kasa, da cewa bawan nan ya garzaya ga sarkin Musulmi, sai sarki ya ce a kyale shi ya tafi abinsa. Wato mai shi ya yi raguwar dabara ke nan, domin da ya bari sun shirya tun a gida tilas ne kuma an yarda bawan nan ya fanshi kansa. Ma' ana, ya rika yin aiki yana samun kudi yana bai wa maigidansa har ya gama fansar kansa. Abin da ya sa maganar bautar nan ta fi karfi a Sakkwato a fili yake. Da farko dai an sha fadar yadda Sauran kasashe ke kai gaisuwar bayi can. Saboda haka babu inda bauta ta yi karfi kamar a Sakkwato. Turawa ka nuna wa jama'a a fili cewa duk wanda yake son 'yanci yana iya samun sa, wanda kuma ya zauna cikin kangin bauta shi ya so.\n Ba a dade da samun galaba kan Sakkwato ba sai aka fara maganar yadda za a jarraba koya wa almajirai karatun Turawa a can. Amma abin bai yi nasara ba. Jama'a suna gani kamar karatun Turawa wani sabon addini ne daban. Saboda haka sai aka yi watsi da lamarin.\n", "mc1_targets": { "choices": [ "Kai gaisuwar bayi can", "Wurin ya fi dacewa da bayi", "An fi kanen bayi a can", "Wurin ya fi kyawun noma" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "Kai gaisuwar bayi can", "Wurin ya fi dacewa da bayi", "An fi kanen bayi a can", "Wurin ya fi kyawun noma" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "“Ita ko bante ta ƙetara sai ta haihu, In ka san kuɗi su ƙare a suna” Wannan tsakure na ‘Waƙar Zambon Ƙazama’ ta Mal. Aliyu Namangi, ta Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Da Da Na Yanzu, na D. Abdulkadir yana Magana ne a kan", "mc1_targets": { "choices": [ "masu gwanne", "tsofaffi", "mata karuwai", "zawarawa" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "masu gwanne", "tsofaffi", "mata karuwai", "zawarawa" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } }, { "question": "Yara masu laƙabi cindo an haife su ne", "mc1_targets": { "choices": [ "da yatsu shida", "lokacin cin doya", "da damina", "ana ruwa" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] }, "mc2_targets": { "choices": [ "da yatsu shida", "lokacin cin doya", "da damina", "ana ruwa" ], "labels": [ 1, 0, 0, 0 ] } } ]